Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana karuwar bashin da Najeriya take ciyowa a matsayin wata babbar matsala ga al’ummar kasar a yanzu da kuma nan gaba.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani shiri mai taken “Boiling Point Arena” da aka gudanar a manhajar Zoom.
A halin yanzu bashin da ake bin Najeriya ya karu da Naira Tiriliyan 12.6 inda ya kai Naira Tiriliyan 134.3 ($91.3bn) a rubu’i na biyu na shekarar 2024. Wannan ya nuna karuwar kashin da kaso 10.35 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira Tiriliyan 121.7 da aka samu a rubu’in farko na shekarar 2024.
Da yake tsokaci kan batun, Obasanjo ya ce, “nayi nasarar gamsar da wasu kasashen su yafewa Najeriya bashin da ta ci a hannun su amma yanayin bashin da ake dada karbowa a yanzu babbar matsalace”
Obasanjo ya buga misali da kasashen Koriya ta Kudu da Singapore a matsayin misali na kasashen da ci gaban da suka samu ya samo asali ne daga shugabanci na gaskiya da rikon amana.
A cewarsa, hanya mafi dacewa ta yaki da cin hanci da rashawa ita ce daga matakin farko na gwamnatin Tarayya har zuwa matakin karshe.
Bashin da Najeriya take karba babbar matsalace ga cigaban kasa – Obasanjo