Hukumar K’kula da ayyukan shari’a ta Jljihar Bauchi ta kori wani alkalin kotun shari’a, Umar Ibrahim, bisa zargin aikata babban laifi.
Alkalin da aka kora yana aiki a Kotun Shari’a ta Jalam da ke karamar hukumar Dambam a jihar.
A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Bauchi, ranar Laraba, shugaban hukumar, Dokta Ibrahim Danjuma, ya ce matakin ya yi daidai da hurumin hukumar na tabbatar da cewa dukkan ma’aikatan shari’a suna bin ka’idojin aiki.
Sanarwar ta ce laifukan da ake zargin alkalin ya aikata sun saba wa dokokin aiki da ka’idojin da suka shafi bangaren shari’a.
“An ɗauki matakan da nufin kare amana da kuma ci gaba da tabbatar da karfin gwmuiwar jama’a ga tsarin shari’a,” in ji sanarwar.
Bauchi: Gwamnati ta kori alkalin kotun shari’ar Muslunci