in

‘Biyan albashin N250,000 ba zai hana rashawa ba – Baffa Babba Dan Agundi

Baffa Babba Dan'Agundi

Shugaban Cibiyar Samar da Ayyuka ta Kasa (NPC), Dr. Baffa Babba Dan’Agundi, ya ce ba lallai ne biyan mafi karancin albashin N250,000 zuwa sama ya dakile cin hanci da rashawa, ko kara kuzarin aiki tsakanin ma’aikatan Najeriya ba.

Ya bayyana cewa ta hanyar biyan alawus-alawus din ma’aikatan , da bayar da ladan aiki ne kawai zai taimaka wajen gyara dabi’un ma’aikata.

Shugaban hukumar NPC ya bayyana haka ne a Abuja yayin da yake ganawa tare da ‘yan jarida game da abubuwan da cibiyar ta cimma a cikin watanni hudu da suka gabata a Abuja.

A cewar Dan’Agundi, ya karbi aikin tare da wasu shirye-shirye da nufin inganta walwalar ma’aikata da kuma karfafa aiki a fannoni daban-daban.

Ya lura cewa ma’aikata ba su fi mayar da hankali ga albashin asali ba, sai dai suna daraja alawusansu da lada na musamman wajen yin aiki yadda ya kamata, ba tare da hakan ba, aikin na saukaka kuma aiyuka suna cikin hadari.

Ya bayyana cewa NPC karkashin jagorancinsa ta gabatar da wasu shirye-shiryen walwalar ma’aikata, ciki har da tsarin ritaya, tallafi na sufuri da kula da lafiya, da kuma gina fasaha don inganta kwarewa da aikin.

Ya bayyana shirin kara inganta samar da aiki a Najeriya, wanda ya hada da; kafa sassan samar da aiki a dukkanin Ma’aikatu, Sassan Ayyuka, da Hukmomin (MDAs), fadada Shirin Inganta Ayyuka da Inganta Inganci (PQIP) domin karfafa kananan masana’antu da kuma kaddamar da samar da aiki a kasa.

‘Biyan albashin N250,000 ba zai hana rashawa ba – Baffa Babba Dan Agundi

Gwamnatin Tarayya ta gargadi Yan kwangilar dake aiki da FERMA su tabbatar sun kammala ayyukansu

Okpebholo gives council chairmen 48-hours to submit statements of account to Assets Verification Committee