Shugaban ƙungiyar ’yan sa-kai da ke tallafawa sojojin Najeriya, Babakura Kolo, ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun kashe mutane 14 masu sana’ar su.
Mutanen da aka kashe sun gudo ne daga yankunan Malam Fatori da Doron Baga a Najeriya saboda tsananin ta’addancin Boko Haram.
Yankin Diffa na Nijar, wanda ke kan iyaka da Najeriya da Chadi, ya dade yana fama da hare-haren Boko Haram da kuma ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP.
Duk da ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi, yankin na cigaba da kasancewa cikin haɗari.
Ɗaya daga cikin membobin Civilian Joint Task Force (CJTF), Ibrahim Liman, ya tabbatar da harin tare da adadin mutanen da suka rasa rayukansu.
Rikicin Boko Haram da ya shafe shekaru 15 a Arewa Maso Gabashin Najeriya ya haifar da mutuwar sama da mutum 400,000 tare da tilasta wa fiye da mutum miliyan biyu barin gidajensu.
Boko Haram sun hallaka masuntan da su ke tsere daga Borno