Jami’an tsaro sun mamaye gidan Sarkin Kano, tare da hana Sarki Muhammadu Sunusi fita don tafiya masarautar Bichi.
Tunda fari masarautar ta tsara cewa Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II zai jagoranci tawaga zuwa raka sabon hakimin Bichi zuwa fadarsa, tare da gudanar da wasu aika-aikace, Sai dai a safiyar yau an wayi gari da ganin jami’an tsaro sun tsare gidan Sarkin.
Tun bayan sauke sarki Aminu Ado Bayero daga karagar mulki a watan Mayu da gwamnatin Kano tayi ta dawo da sarki Muhammadu Sanusu kan karaga aka fara fuskantar tataburza game da wanene halastaccen sarki a tsakanin su biyun.Hakazalika, an shigar da shari’a a kotuna daban daban don tantance hakan.
Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumace game da halin da ake ciki daga masarautar ko gwamnatin Kano, suma jami’an tsaron basu fitar da wani bayani ba akan hakan.
Da Dumi-Dumi: Jami’an tsaro sun mamaye gidan sarkin Kano