in

Dakatar da aikin hanyar Kano-Abuja babban koma baya ne – Shugaban NANS

Shugaban Kungiyar Dalibai ta Ƙasa (NANS) Yankin A, Sadi Garba Said, ya bayyana matuƙar takaicinsa da damuwa kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na dakatar da aikin gina hanyar Kano-Abuja.

Mal. Sa’id yana mai cewa wannan mataki babban koma baya ne ga al’ummar yankin.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa.

Sadi ya ce, “Dakatar da wannan aiki zai shafi tattalin arziki da walwalar jama’a sosai, kuma hakan yana nufin ƙarin wahala ga matafiya.”

Aikin, wanda aka fara tun 10 ga Fabrairu, 2021, an shirya kammala shi a ƙarshen 2023. Amma dakatarwar da aka yi kwatsam ta haifar da matsaloli, inda matafiya suka fara fuskantar wahalhalu irin su tsawaitar tafiya da tsadar sufuri.

Sadi ya nuna damuwa kan yadda dalibai da ke amfani da hanyar don zuwa makaranta ke fuskantar ƙalubale. “Daliban da ke dogaro da wannan hanya don tafiye-tafiye sun shiga halin ha’ula’i. Wannan yanayi ba zai iya ci gaba haka ba,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske kan dalilin da ya sa aka dakatar da aikin tare da Julius Berger Nigeria Plc, tare da bayyana sabon shiri mai kyau na kammala aikin.

“Ba za mu yarda da ƙarin jinkiri ba. Gwamnati dole ta nuna gaskiya da amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace,” Sadi ya jaddada.

Haka kuma, ya yi alkawarin cewa NANS Yankin A za ta ci gaba da sanya ido kan wannan lamari domin kare haƙƙi da walwalar al’umma. “Zamu tabbatar gwamnati tana cika alƙawuran da ta ɗauka kan wannan aiki domin ci gaban al’ummar mu,” ya ƙara da cewa.

Dakatar da aikin hanyar Kano-Abuja babban koma baya ne – Shugaban NANS

NPFL: Okwuchukwu keen to face former club, Abia Warriors

EPL: 3 matches we could see shock results this weekend