in

Dan takarar Majalisar Wakilai ya fice daga jam’iyyar ADC

Tsohon Daraktan Yunkurin Matasa kuma dan takarar Majalisar Wakilai na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a mazabar Ningi/Warji ta Jihar Bauchi a zaben 2023, Zakari Garba, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a ranar Litinin.

Ficewar tasa ta fito ne a wata wasika mai kwanan watan 8 ga Disamba, wacce aka aikawa Shugaban Kasa na ADC, Cif Okey Nwosu.

A cewarsa, ya yanke wannan hukuncin ne saboda rashin daidaiton ra’ayi da dabi’u tsakaninsa da jam’iyyar ADC.

Ya ce, “Ina sanar da ku da kuma jama’a cewa na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) daga ranar 8 ga Disamba, 2024. Wannan shawara ba ta zo mini da sauki ba, amma na ga ya zama dole saboda burina na siyasa.”

“Ina matukar godiya da goyon baya da jagorancin da na samu a karkashin jam’iyyar, tare da yabawa damar da aka ba ni don taka rawa a fagen siyasa.

“Amma yanzu na fahimci cewa ra’ayina da dabi’una ba su yi daidai da manufofin jam’iyyar ba. Saboda haka, na yanke shawarar fita daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).”

Yayin da yake yabawa goyon bayan magoya bayansa masu tarin yawa, Garba ya ce zai sanar da matakin siyasa na gaba da zai dauka nan gaba kadan.

Dan takarar Majalisar Wakilai ya fice daga jam’iyyar ADC

MDD ta bukaci a dauki matakin gaggawa kan cin zarafin mata a Najeriya

Turkey: Injured Osimhen set for spell on sidelines