Shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar Laraba cewa bukatun da jin dadin ‘yan kasashen Mali, Burkina Faso, da Niger na ci gaba da kasancewa manyan batutuwan da shugabannin ECOWAS ke mayar da hankali a kai.
A wajen taron da ya yi da Shugaban Jamus, Frank-Walter Steinmeier, a ziyarar da yake gabtarwa a fadar Shugaban Kasa, dake Abuja.
Tinubu, wanda kuma shi ne Shugaban ECOWAS, ya bayyana cewa kasashen uku na cikin matsala wajen shirye-shiryen mika mulki ga farar hula.
Shugaba Tinubu ya ce shugabannin ECOWAS suna mai da hankali wajen ganin cewa kasashen da suka fuskanci juyin mulki na dawo dawowa kan tsarin mulkin dimokuradiyya cikin gaggawa.
A cewar Tinubu, wannan aiki yana buƙatar haɗin kai, hikima, da kuma amfani da hanyoyin diplomatik don cimma nasara. Ya kuma yi alkawarin cewa za a yi amfani da hikima da dabaru na diplomasiya don tabbatar da cewa kasashen Mali, Burkina Faso, da Niger sun sake komawa cikin kungiyar ECOWAS.
ECOWAS ta tattauna bukatun kasashen Sahel 3