Wasu mutane shida sun rasa rayukansu, sannan wasu mutum takwas sun ji munanan raunuka, bayan da motarsu ta taka wata nakiya a jihar Zamfara.
Ana zargin yan bindiga ne suka dasa bam din a kan hanyar zuwa garin Dansadau, a yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Mazauna garin Dansadau sun tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, inda suka ce motar fasinja mai kirar Golf na tafiya a lokacin da ta taka nakiyar.
Sun bayyana cewa wannan ya jawo hadari mai muni ainun, tare da yin fata-fata da motar har wasu su ka rasa rayukansu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, suna cikin fargaba game da wannan sabon salon kai hari da ‘yan bindiga ke amfani da shi, wanda ke nufin hana jami’an tsaro kai musu hari, kuma yana zama wani mataki na kashe jama’a musamman matafiya.
Har yanzu gwamnatin jihar Zamfara da rundunar ‘yan sanda ba su ce komai ba a kan wannan al’amari.
Fasinjoji 6 sun rasu bayan taka bam a jihar Zamfara