in

Fiye da 70% na ayyukan gwamnati a Kaduna sun zama na zamani, in ji kwamishina

Kwamishiniyar kirkire-kirkire a kasuwanci da fasaha ta Kaduna, Patience Fakai, ta ce fiye da kashi 70% na ayyukan gwamnati yanzu an sauya su zuwa tsarin zamani.

Da take magana da manema labarai a ranar Talata, Fakai ta bayyana cewa jihar ta kaddamar da haɗaɗɗen tsarin gudanar da gwamnati a zamanance a matakin jiha da kananan hukumomi.

Ta ce gwamnatin Uba Sani ta inganta yadda ake gudanar da mulki da sauƙaƙe samun ayyukan gwamnati ta hanyar wani ingantaccen tsarin sadarwa na cikin gida da ke tallafawa sadarwa da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi.

Kwamishiniyar ta kara da cewa Jihar Kaduna ta zama ta uku a rukunin ci gaban ɗan adam ta fuskar fasahar sadarwa a taron majalisar kasa na 12 kan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arzikin zamani da aka gudanar makon da ya gabata a Makurdi.

“Fiye da kashi 70% na ayyukan gwamnati a jihar Kaduna yanzu an sauya su zuwa tsarin zamani karkashin gwamnatin Uba Sani, wanda hakan ya kara inganci da samun damar yin amfani da bayanan gwamnati,” in ji ta.

“Shafin yanar gizon jihar, www.kdsg.gov.ng, yana aiki sosai, kuma yana matsayin cibiyar samun bayanai ga jama’a,” inji kwamishiniyar.

Fiye da 70% na ayyukan gwamnati a Kaduna sun zama na zamani, in ji kwamishina

Hukumar Hisbah a Sokoto ta kwace katan 200 na barasa

North-West stakeholders urge Tinubu to reconsider SMDF/PAGMI Executive Secretary appointment