in

Gammayar jami’an tsaro sun ceto manoma 36 da akayi garkuwa dasu a Kebbi

Rundunar ‘yan sanda da hadin gwiwwar sojoji da ‘yan banga sun ceto wasu manoma 36 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Mairairai/Bena da ke karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun tare hanyar Mairairai/Bena inda suka yi garkuwa da wasu manoma 36 da suke dawowa daga gonakinsu a yankin.

“An tattaro jami’an tsaron na hadin gwiwa zuwa wurin inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan. Rundunar ta ci galaba a kan ‘yan bindigan da suka tsere zuwa cikin dajin da raunukan harbin bindiga. An ceto manoma 36 ba tare da sun samu wani rauni ba, kuma tuni suka koma gida wajen iyalansu” in ji sanarwar.

Hakazalika, kwamishinan ‘yan sandan, Bello M. Sani ya yabawa jarumtakar da jami’an suka nuna ya kuma hore su da kara jajircewa wajen ganin jihar Kebbi ta zauna lafiya.

Gammayar jami’an tsaro sun ceto manoma 36 da akayi garkuwa dasu a Kebbi

Dele Farotimi: Sowore condemns Peter Obi’s visit to Afe Babalola

Nigeria maintains clean slate on blocked airlines’ funds — IATA