Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya John Dramani Mahama murna bisa lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar a Ghana.
Sakon taya murnar na kunshe a cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, a ranar Lahadi, a birnin Abuja.
A cewar sanarwar, Tinubu, cikin wata hira ta waya da Mahama, ya nufatan cewa dawowar Mahama karagar mulki karo na biyu zai ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
Tinubu ya yabawa al’ummar Ghana bisa jajircewarsu kan kare dimokuraɗiyya, wanda suka nuna ta hanyar gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Shugaban Najeriya ya ce mazauna Ghana sun sake nuna wa duniya cewa dimokuraɗiyya ce hanya mafi dacewa don cimma cigaban siyasa, ci gaban tattalin arziki, adalci a zamantakewa, da shugabanci nagari a nahiyar Afirka.
Tinubu ya yaba wa Dr. Mahamudu Bawumia, ɗan takarar NPP, mai mulki kuma mataimakin shugaban ƙasa na Ghana, bisa amincewa da shan kaye a zaɓe tun kafin sanarwar hukuma daga hukumar zaɓen Ghana.
Ya ce irin wannan matakin na Bawumia ya tabbatar da ƙwarin gwiwar da ake da shi a kan dimokuraɗiyya.
Tinubu ya kuma bayyana cewa dawowar Mahama zuwa fadar Jubilee, bayan mulkinsa na farko daga 2012 zuwa 2017, ya nuna amincewar jama’ar Ghana ga jajircewarsa da hangen nesansa na ɗaga martabar ƙasar zuwa matakin ci gaba.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Shugaba Tinubu ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga ƙara ƙarfafa alaƙar ƴan’uwantaka tsakanin Najeriya da Ghana, wadda ta samo asali daga tarihi, alaƙar al’adu, goyon baya da haɗin kai, dimokuraɗiyya, bin doka, da haɗin kan tattalin arziki.”
Tinubu ya kuma gode wa Shugaba Nana Akufo-Addo saboda jagorancinsa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Ghana da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ghana: Tinubu ya taya Mahama murnar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa