Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane shida zuwa ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa a matsayin sabbin kwamishinoni na ma’aikatu daban-daban.
Matakin ya biyo bayan sauye-sauyen da gwamnan ya yi a majalisar zartarwarsa, inda wasu tsoffin kwamishinoni suka rasa mukamansu, wasu kuma aka sauya musu ma’aikatu.
Sunayen mutanen da aka miƙa don tantancewar sun hada da: Alhaji Shehu Wada Sagagi, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam,Ibrahim A. Waiya,Dr. Isma’il Danmaraya,Dr. Ghadafi Sani Shehu,Dr. Dahir M. Hashim.
A halin yanzu, ma’aikatun raya karkara, kudi, muhalli, yada labarai, al’amuran jin kai, da wutar Lantarki basu da kwamishinoni.
Majalisar dokokin jihar ta bukaci mutane shidan su gabatar da takaddun karatunsy don za ta fara tantance su kafin su fara aiki.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika sunayen sabbin kwamishinoni ga majalisa don tantancewa