Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci daliban da gwamnatinsa ta dauki nauyin su karo karatu a kasar India.
A ziyarar da ya kai kasar a ranar Talata, gwamna Yusuf ya yaba da yadda daliban su ka mayar da hankali wajen karatunsu.
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai.
Gwamnan ya ce daliban sun kara masa kwarin gwiwa, domin ba a yi asarar kudin tara ba.
Ya dauki alkawarin gwamnatinsa, za ta cigaba da inganta harkar ilimi domin amfanin mutanen jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma shawarce su da kara kwazo domin inganta ilimin da su ka je nema.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci daliban da gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatunsu a India