in

Gwamna Abba zai biya kudin karatun daliban Kano da Ganduje ya manta da su a Cyprus

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki alkawarin biya wa daliban da ba su samu takardun shaidar kammala karatunsu ba yayin mulkin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin, an bayyana cewa gwamna Yusuf ya yi wata muhimmiyar ganawa da mahukuntan Near East University da ke Cyprus domin tattauna batun.

Ganawar ta mayar da hankali kan sakin takardun shaidar karatun daliban Kano da suka kammala karatunsu daga shekarar 2015 zuwa 2019.

Da dama daga cikin waɗannan daliban, musamman daga fannonin Likitanci da Jinya, ba su samu damar ci gaba da aikinsu ba saboda gazawar gwamnatin Ganduje wajen biyan kudin makaranta.

Gwamnan ya bayyana wannan matsala a matsayin babbar koma-baya, ba ga daliban kawai ba, har ma ga jihar Kano, wadda ta rasa kwararru a bangarori masu muhimmanci.

Sai dai, ya nuna gamsuwa bayan tattaunawa da mahukuntan jami’ar, inda aka tsara hanyoyin biyan bashin da ake bin gwamnatin jihar da kuma sakin takardun daliban.

Gwamna Abba zai biya kudin karatun daliban Kano da Ganduje ya manta da su a Cyprus

Simbo Olorunfemi: Is the Port Harcourt Refinery now born again?

Taraba communities urge lawmaker to address infrastructure challenges