Gwamnan jiar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya rantsar da sabbin alkalan babbar kotun jihar guda hudu da manyan Khadi guda biyu.
Taron rantsuwar ya gudana ne a adar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, a ranar Juma’a.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya gabatar da sunayen sabbin alkalai hudu kamar haka: Mai Girma Hassan Kwaido, Halima Umar Ibrahim, Lauratu Jagwadeji Suru, da Muhammad Nurudeen.
Haka kuma ya gabatar da sunayen Khadi guda biyu da suka hada da Kabiru Aliyu, SAN, da Atiku Muhammad Bello daga kotun shari’a.
A jawabinsa, Gwamna Nasir Idris ya bayyana farin cikinsa tare da taya wadanda aka rantsar murna.
Ya yi alfahari da samun dama ta musamman na rantsar da sabbin jami’an shari’a guda shida.
Gwamnan ya yaba wa Ma’aikatar shari’a ta jihar saboda kokarinta wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da biyan albashi da kula da jin dadin Alkalai a jihar.
“Ina kuma yaba wa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar saboda jajircewarta wajen sauke nauyin da ke kanta. Har ila yau, a karkashin wannan gwamnati, ba mu taba samun tangarda daga gare ku ba,” in ji sanarwar Yahaya Sarki, mashawarci na musamman ga Gwamna Nasir Idris.
Haka kuma, Gwamnan ya sanar da amincewarsa da biyan N300m don sayen motocin aiki ga alkalai.
Ya shawarci sabbin jami’an da su yi amfani da kwarewarsu tare da kiyaye ka’idodin aikin shari’a.
Gwamna Idris ya rantsar da sabbin alkalai, za a saya masu motocin N300m