Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya nada shahararren jarumi a masana’antar Kannywood Sani Musa Danja a matsayim mai nashi shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi, tace nadin ya fara aiki ne nan take.
Gwamnan ya kuma amince da nada wasu sabbin mataimaka da masu bashi shawara, sannan an.nada Dr Ibrahim Musa a matsayin mai duba lafiyar gwamnan kuma mashawarci kan sha`anin lafiya.
Sauran wadanda aka nada sune :
Dr. Hadiza Lawan Ahmad – Mai Ba Da Shawara na Musamman, Zuba Jari da Hadin Gwiwa Tsakanin Gwamnati da Masana’antu.
Barr. Aminu Hussain – Mai Ba Da Shawara na Musamman, Shari’a/Al’amuran Kundin Tsarin Mulki
Dr. Ismail Lawan Suleiman – Mai Ba Da Shawara na Musamman, Yawan Al’umma
Nasiru Isa Jarma – Mai Ba Da Shawara na Musamman, Kungiyoyi na Gida
Hon. Wada Ibrahim Daho – Kwamishina na Daya, SUBEB
Hon. Ado Danjummai Wudil – Sakatare Janar, Hukumar Koyar da Shawara
Dr. Binta Abubakar – Sakatare Janar, Hukumar Ilimi na Jama’a
Hon. Abubakar Ahmad Bichi – Darakta Janar, Hukumar Kula da Kananan Harkokin Kasuwanci da Sana’o’in Tituna
Hon. Abdullahi Yaryasa – Memba, Hukumar Kula da Harkokin Majalisar Dokokin Jihar Kano
Dr. Yusuf Ya’u Gambo – Shugaban Hukumar Kula da Tsarin Mulki da Tsare-Tsare
Gwamna Kano ya yi sabbin nade-nade, dan Kanywood ya samu mukami