Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da ƙudurin kafa wasu masarautu uku masu daraja ta ɗaya a jihar.
Dokar, wadda yanzu ke jiran sa hannun gwamna, Ahmadu Finitiri, na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya sanya hannu kan wata dokar ta ƙirƙirar gundumomi 84.
A wata wasiƙa da gwamna ya aikawa majalisar, ya buƙaci a amince da ƙudurin naɗawa da cire sarakunan jihar, wadda za ta ba shi damar ƙirƙirar sababbin masarautu, naɗa sarakuna da cire su.
Ƙudurin ya tsallake karatu na farko da na biyu a majalisar a ranar Litinin, sannan a ranar Talata ƴanmajalisar su ka amince da shi, inda yanzu ake jiran sa hannun gwamna domin ya zama doka.
Sabuwar dokar, ta cire wa Lamiɗon Adamawa, Mustapha Barkindo, muƙaminsa na shugaban majalisar sarakunan Adamawa na dindindin, inda yanzu zai riƙa zagawa tsakanin sarakunan jihar masu daraja ta ɗaya.
Sannan a doka ta farko da gwamnan ya sa hannu, an rage ƙasar Lamidon Adamawa daga ƙananan hukumomi takwas zuwa uku.
Gwamnatin Adamawa ta rage wa Lamido mukami, zata kirkiro sabbun masarautu