in

Gwamnatin Bauchi ta shirya tabbatar da hakar fetur a filin mai na Kolmani

Gwamnatin jihar Bauchi ta sake tabbatar da goyon bayanta ga cimma nasarar haƙar mai a filin man Kolmani, tana mai alkawarin bayar da dukkan tallafin da ake bukata domin nasarar aikin.

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Jatau, ya bayar da wannan tabbacin a ranar Litinin yayin da yake ganawa da manema labarai a lokacin ziyarar gani da ido da ya kai filin man Kolmani tare da mambobin kwamitin mai na hukumar rarraba kudaden shiga da tattalin arziki (RMAFC).

Jatau ya jaddada shirye-shiryen gwamnatin jihar na yin aiki tare da gwamnatin tarayya, kamfanin NNPCL da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa filin mai na Kolmani ya zama cikakken mai aiki, wanda zai amfani jihar, makwabtan jihohi, da ƙasa baki ɗaya.

“A matsayinmu na gwamnati, mun riga mun tabbatar wa gwamnatin tarayya da duk wanda ke aiki a nan, ko kamfani ne ko ƙungiyoyi, da cikakken goyon bayanmu, ta fuskar tsaro, kayan more rayuwa, ko harkokin sufuri.

“Wannan shi ne matsayarmu tun lokacin da aka samar da filin man Kolmani har zuwa yau,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, Abdulhamid Aminu, wakilin kamfanin gine-gine na Sterling Global, ya bayyana cewa ana mai da hankali kan haƙar rijiyoyi biyu na mai don ƙarfafa rijiyoyin PL809 da OPL810 da ke wajen.

Ya kuma bayyana cewa fara ɗaukar danyen mai daga wurin zai ta’allaka da kammala waɗannan sabbin rijiyoyi.

Gwamnatin Bauchi ta shirya tabbatar da hakar fetur a filin mai na Kolmani

Adamawa plans grazing reserves to curtail clashes between herders, farmers

Buba Galadima ya zargi APC da kokarin mallake ‘yan adawa