Gwamnatin jihar Jigawa ta gano ma’aikatan bogi 6,348 yayin binciken tantance ma’aikata da aka gudanar a jihar.
Kwamishinan Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Malam Sagir Musa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Dutse.
Ya ce rahoton binciken ma’aikata na jiha da kuma rajistar tantance bayanan su ya nuna an gano ma’aikata 6,348 na bogi,
Musa ya bayyana cewa Majalisar Zartarwar Jihar ta duba rahoton sannan ta amince da kafa Cibiyar cigaba da Rijista (CCC) a ofishin Shugaban Ma’aikata na Jiha.
“Wannan matakin zai hanzarta kammala rijista da tantance ma’aikata a karkashin tsarin Integrated Payroll and Personnel Management System (IPPMS),” inji shi.
Musa ya ce aikin ya ragewa gwamanti kashe kudi da kimanin N314,657,342.06 a kowane wata da kuma N3,775,888,809.72 a shekara.
Har ila yau, kwamishinan ya ce majalisar ta amince da kwangilar gyaran hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata, wanda ya hada da hanyoyin Andaza – Gadewa – Aujara; Unguwar Mani – Korayel – Rorau da Tsamiya – Yalwan Damai – Litinin Tudu a kananan hukumomin Roni, Gwiwa, da Birnin Kudu.
Sannan majalisar ta amince da kashe N254.8 miliyan don kammala shigar da al’ummomi cikin tsarin Rijistar jinkai na Jiha.
“Wannan matakin ya yi daidai da kokarin gwamnatin Umar Namadi na fadada tsarin walwala zuwa al’ummomin da ba su cikin rijistar walwala,” inji Musa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da aiwatar da shawarwarin kwamitin kwato filayen noma da aka rarraba a fadin jihar.
Gwamnatin jihar Jigawa ta gano ma’aikatan bogi 6,348