in

Gwamnatin Kaduna ta shirya taron gina kwarewa ga ma’aikata

Jihar Kaduna na da daya daga cikin mafi ingancin ma’aikatan gwamnati a Najeriya, inda jihohi daban-daban ke tura wakilai don koyon yadda take gudanar da ayyukanta, musamman wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.

An bayyana hakan yayin wani taron bita na kwana biyu kan gina ƙwarewa, wanda ofishin Shugaban Ma’aikata tare da Babban Sakatare na Musamman ga Gwamna Uba Sani suka shirya, daga ranar 4 zuwa 5 ga Disamba.

Takardar bayanin da aka fitar bayan taron ta bayyana cewa Ma’aikatan Gwamnatin Kaduna suna gudanar da ayyukansu ne bisa ka’idoji kamar “Tsarin Aiki,” “Dokokin Kula da Kaya,” “Dokokin Gudanar da Kudi,Jagorar Hanyoyin Gudanar da Ayyuka,” da “Financial Instructions.”

Takardar bayanin ta ba da shawarar cewa Sashen Buga Takardu ya samar da waɗannan Littattafan Dokoki/Ka’idoji tare da siyar da su ga ma’aikatan gwamnati a farashi mai sauƙi.

Takardar bayanin, wadda Alhaji Waziri Garba, Mataimakin Musamman na Shugaba kan Harkokin Gudanarwa, da Malam Ibraheem Musa, Babban Sakataren Yaɗa Labarai, suka sanyawa hannu tare, ta bayyana cewa taron gina ƙwarewa an shirya shi ne musamman don ma’aikatan Fadar Gwamnati.

Masu halartar taron sun yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani bisa shirya wannan taron, wanda suka bayyana a matsayin “na farko irinsa a tarihin jihar”

Gwamnatin Kaduna ta shirya taron gina kwarewa ga ma’aikata

‘Yan adawar Siriya sun sanar da hambarar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad

Yuletide: NAFDAC warns Nigerians against fake drinks