Gwamnatin Kano ta ba da kyautar kujerun hajji tare da kuɗi sama da Naira miliyan biyu ga mutane 2 da suka yi nasara a gasar karatun Alkur’ani da ake gudanarwa duk shekara a jihar.
Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam gwarzo ne ya bayyana hakan a wajen bikin rufe gasar da aka gudanar a makarantar koyon harshen harshen Larabci ta SAS dake birnin Kano a safiyar Talata.
Da yake jawabi ya yin rufe taron musabakar alkur’anin mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya yabawa jagororin musabakar, sannan ya jaddada ƙudirin gwamnatin Kano na cigaba da tallafawa karatun Alkur’ani a jihar nan baki daya.
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana ce wa gwamnati zata ci gaba da marawa wadanda su ka yi nasara baya a gasar da za’ayi a matsayin tarayya.
Da yake nasa jawabin, Sarkin Kano 16, Muhammadu Sanusi II yabawa daliban da suka samu nasara a musabakar, sannan yaja hankalinsu da suyi kokari su zama zakaru a gasar da za’ayi.
A nasa jawabin, Malam Nasidi Abubakar Goron Dutse ya ja hankalin daliban da su tsarkake niyyarsu don samun rabo mai girma a ranar alkiyama.
Gwamnatin Kano ta yi kyautar kujerun hajji ga zakarun musabaƙa