Gwamnatin Jihar Kebbi zata fara ba iyayen da suka amince ayi wa yaransu allurar rigakafin cutar shan inna na goro.
Gwamna Nasir Idris ne ya bayyana haka a wajen taron kaddamar da shirin allurar rigakafi a birnin Kebbi
Gwamnan yace jihar ta samu nasarar kakkabe cutar a baya tun daga shekarar 2011, sai dai ana cigaba da daukar matakai domin ganin ba a sake samun rahoton bullarta ba.
“Ina godewa ma’aikatan lafiya wadanda jajircewar su ce ta kaimu ga wannan nasara” inji Gwamna Nasir Idris
Mai martaba Sarki Argungun, Dr Sama’ila Mohammed Nera wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar yayi kira ga al’umma musamman a karkara da su dage wajen kai yaransu allurar rigakafin
Gwamnan ya bawa hakimai da dagatai da iyayen yara da suka kai yayansu kyautar naira mikiyan 5 nan take.
Gwamnatin Kebbi ta kaddamar da rigakafin cutar shan inna