Gwamnatin Tarayya ta fara gina hedkwatar ‘Yan Sanda ta zamani a Mpape, wani yanki a Karamar Hukumar Bwari na Abuja, tare da gina gidaje guda shida ga jami’an ‘Yan Sanda masu matsayi na kasa.
Wannan aikin na daga cikin shirye-shiryen gyaran tsarin ‘yan sanda, wanda aka kaddamar domin inganta aikin.
An gudanar da aikin asasa sabon tashar ‘yan sanda ta zamani ne da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Ibrahim Gaidam, wanda wakiltarsa yayi da Ma’aji mai gudanar da ayyuka na ma’aikatar, Yusuf Argungu.
Ya nuna cewa wannan aikin zai samar da yanayi mai kyau da kuma tsaro ga mazauna da masu kasuwanci a yankin.
Ministan ya ce: “Samuwar wannan hedkwatar ‘yan sanda a wannan wuri zai kare ‘yan kasa da ke tafiye-tafiye kullum daga hadurran satar mutane, ayyukan kwace (‘one-chance’), da fashi da makami, da sauran laifukan da ke addabar al’umma a cikin birnin.”
Gwamnatin tarayya ta fara gina ofisoshin ƴansanda na zamani a Abuja