in

Gwamnatin tarayya ta fara jigilar fasinjojin jrgin kasa kyauta

Gwamnatin Tarayya ta fara jigilar fasinjoji kyauta ta jiragen ƙasa a faɗin Najeriya, da nufin rage wa jama’a wahalar sufuri yayin bukukuwan Kirsimeti.

Muƙaddashin Manajan Daraktan Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC), Ben Iloanusi, ya yi maraba da fasinjojin farko da suka iso tashar jirgin ƙasa ta Kubwa, Abuja, daga Rigasa, Kaduna.

Iloanusi Ya bayyana damuwa kan batun kare lafiyar fasinjoji a wannan rana ta farko, tare da tabbatar da cewa Hukumar na ɗaukar matakai don magance matsalolin tsaro da ka iya tasowa.

A cewarsa, shirin jigilar kyauta zai ɗauki fasinjoji kusan 20,000 a kullum, tare da kiyasin jigilar fasinjoji har 340,000 kafin wa’adin shirin ya ƙare a makon farko na watan Janairu.

Gwamnatin tarayya ta fara jigilar fasinjojin jrgin kasa kyauta

‘We’ll fight hard to escape relegation’—Akwa United

EPL: ‘He’s top player’ — Cucurella hails Chelsea youngster