in

Gyare-gyaren haraji na iya jefa Jihohi cikin matsala – Gwamna Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce wasu jihohin da ba su da ƙarfin tattalin arziki na iya fuskantar ƙalubale idan an amince da sabbin dokokin haraji da ke gaban Majalisar Ƙasa kuma Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu a kansu.

Gwamnan ya bayyana hakan a cikin shirin Politics Today na Channels Television ranar Talata, inda ya ce dole ne a yi nazari sosai kan wannan batun don guje wa matsaloli nan gaba.

Gwamna Dauda Lawal ya ce batun haraji yana da bangarori biyu, masu kyau da marasa kyau, kuma suna kan nazarin lamarin domin su bawa al’ummarsu shawara kan matakin da ya dace a gaba.
Ya ce tattaunawa kan batun na ci gaba kuma za su ci gaba da shiga cikin shawarwari.

Ya ce, “Aiwatar da sabbin gyare-gyaren haraji na iya sanya jihohi da yawa cikin wahalar biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.”

Sabbin kudirorin haraji da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar sun haifar da cece-kuce a fadin ƙasa, tare da fuskantar suka daga wurare daban-daban, ciki har da gwamnoni 36 a ƙarƙashin Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC).

Haka kuma, gwamnoni 19 na Arewa sun koka da wasu sassa na dokokin.

Gyare-gyaren haraji na iya jefa Jihohi cikin matsala – Gwamna Lawal

Nigerians now run to VDM for help instead of government – Skales laments

WHO approves Codix group package prequalified rapid diagnostic test in Nigeria