Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya ta nada Ajibogun Olatubosun a matsayin sabon Mai Kula da Hukumar Gyaran Hali ta Babban Birnin Tarayya.
An bayyana wannan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Adamu Duza, ya sanya hannu a ranar Laraba.
Olatubosun ya karbi ragama daga Controller Usman, wanda aka mayar da shi zuwa Zone ‘R’ a Maiduguri a matsayin Acting Zonal Coordinator.
A lokacin taron mika ragamar ranar Talata, Usman ya yabawa ma’aikatan Hukumar Gyaran Hali ta FCT saboda sadaukarwarsu da jajircewarsu, yana bayyana tabbacin sa a kan iyawarsu wajen gudanar da kowanne aiki da aka dora musu.
Haka kuma, ya bayyana fata cewa Olatubosun zai kara inganta aikin Hukumar.
A cikin maganarsa, Olatubosun ya gode wa Allah saboda damar da aka bashi na yin aiki a sabon matsayinsa, sannan ya roki ci gaba da hadin kai wajen tabbatar da nasarar Hukumar.
Hukumar gyara hali ta FCT ta samu sabon mai kula