in

Hukumar Hisbah a Sokoto ta kwace katan 200 na barasa

Jami’an hukumar Hisbah a jihar Sokoto sun kwace fiye da katan 200 na abubuwan da ake zargin barasa ne a babbar tashar mota ta jihar.

Kwamandan Hisbah na jihar, Usman Jatau, ya sanar da hakan a lokacin da yake bayyana kayayyakin da aka kwace yayin taron da ya yi da manema labarai a ofishin hukumar a Sokoto, ranar Laraba.

Jatau ya bayyana cewa, duk da cewa an kwace kayayyakin, babu wanda ya bayyana cewa kayan mallakinsu ne. Saboda haka, hukumar ta yanke shawarar tuntuɓar kwamishinan shari’a da babban lauyan jihar domin sanin matakan da za a dauka na gaba.

Hukumar Hisbah a Sokoto ta kwace katan 200 na barasa

Babu kowa a kujerar Sanatan Edo ta Tsakiya – Apkabio

Fiye da 70% na ayyukan gwamnati a Kaduna sun zama na zamani, in ji kwamishina