in

Jami’an tsaro sun hana yan jarida shiga gabatar da kasafin kudin gwamnan Zamfara

Jami’an tsaro sun hana yan jarida shiga majalisar dokokin jihar Zamfara a lokacin da gwamna ya ke gabatar da kasafin kudin 2025 a ranar Alhamis.

Yan jaridar sun isa majalisar dokoki da ke Gusau don halartar taron da aka shirya farawa karfe 10:00 na safe, amma jami’an tsaro sun hana su shiga.

Jami’an tsaron sun rufe dukkan kofofin shiga dakin taron tare da tsaurara matakan hana ‘yan jaridar shiga, duk da kokarin da mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya yi don shawo kan su.

Idris ya yi roko ga jami’an tsaron, amma ba su saurare shi ba.

Wani jami’in DSS, wanda ya jagoranci jami’an tsaron, ya bayyana karara cewa ba za a bari ‘yan jarida su shiga dakin taro ba. Har ila yau, ya umarci jami’ansa su tabbatar da cewa kofofin sun kasance a kulle.

Wata majiyar a majalisa dokoki ya bayyana cewa wannan mataki na jami’an tsaron na da alaka da rashin cikar kason da ake bukata na mambobin majalisar don gudanar da taron.

“Tabbas, ana sane aka dauki matakin sanoda yawan jami’an tsaron da aka jigbe a wajen,” in ji majiyar.

Ya kara da cewa daga cikin mambobin 24 na majalisar, takwas kawai suka halarci taron.

Jami’an tsaro sun hana yan jarida shiga gabatar da kasafin kudin gwamnan Zamfara

54,000 women benefit from N3bn individual livelihood grants – Ogun Deputy Governor

Za a kara yawan makarantun horar da yan sanda