in

Jami’ar ATBU ta dage ranar dawowa zangon karatun 2024/2025

Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi (ATBU) ta dage ranar dawowa zangon karatun dalibai na shekarar 2024/2025.

Tun da fari jami’ar ta shirya ci gaba da sabon zangon karatun a ranar 6 ga watan Disamba. Sai dai ATBU a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya dauke da sa hannun daraktan yada labarai Zailani Nappa, ta ce za a fara zangon karatun 2024/2025 a watan Janairun shekara mai zuwa.

“Mahukuntan Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, na son sanar da dage ranar ci gaba da karatun zangon farko na 24/2025 zuwa ranar 6 ga Janairu, 2025,” in ji sanarwar.

Nappa ya kara da cewa yanke shawarar dage komawa aiki ya zama dole saboda samun kai a wani yanayi da ba’a shirya tunkararsa ba.

Ya kara da cewar “Hukumar makaranta ta yi nadamar duk wata matsala da sauyin ranar komawar ke ka iya haifar wa”

Jami’ar ATBU ta dage ranar dawowa zangon karatun 2024/2025

NNPC ta kaddamar da jarabawar CBT ga masu neman aiki

Jinkirin Jirage: Najeriya za ta hukunta kamfanonin jiragen sama masu laifi