in

Kaduna – Gwamnati ta gargadi masu rike da mukaman siyasa a kan amfani da shafukan zumunta

An gargadi masu rike da mukaman siyasa a jihar Kaduna da su guji wallafa sakonnin da ba su dace ba a kafofin sada zumunta, saboda irin wadannan sakonni na iya janyo mummunar fahimta ga gwamnati.

Wannan gargadin ya fito ne daga wata sanarwa da aka bayar bayan kammala taron karawa juna sani na kwanaki biyu wanda ofishin shugaban na’aikata da sakatare na musamman ga gwamna Uba Sani suka shirya, daga ranar 4 zuwa 5 ga Disamba.

Sanarwar da suka sanya wa hannu tare, Alhaji Waziri Garba, mataimaki na musamman kan harkokin gudanarwa, da Malam Ibraheem Musa, babban sakataren yada labarai, ta bayyana cewa aikin ma’aikatan jihar Kaduna yana tafiya ne bisa doka.

“An shawarci masu rike da mukaman siyasa da su guji wallafa sakonnin da ba su dace ba a kafofin sada zumunta saboda irin wadannan maganganu na iya janyo mummunar fahimta cewa ra’ayin gwamnati ne, wanda hakan zai iya haifar da matsaloli ko kuma tada hankalin jama’a.”

Kaduna – Gwamnati ta gargadi masu rike da mukaman siyasa a kan amfani da shafukan zumunta

Why I can’t be victim of paternity fraud – Blaqbonez

Police foil two kidnap attempts in Katsina, rescue 20