in

Kano Pillars na fatan nasara a wasanta da Shooting Stars

Kocin Kano Pillars, Usman Abdallah, yace yana da kwarin gwiwar cewa tawagarsa za ta iya shawo kan matsalar rashin wasu muhimman ‘yan wasa a wasan da za su buga da Shooting Stars.

Kungiyar ta Sai Masu gida, za ta kasance ba tare da muhimman ‘yan wasa takwas ba a wasan.

Captain Ahmed Musa, Shehu Abdullahi, Zulkifilu Muhammed, da Sudais Ali Baba duk suna fama da raunuka.

Sauran sune Rabiu Ali, Nelson Abiam, da Aminu Adam Sani suna ci gaba da wakiltar ƙasar nan.

Shi kuwa mai tsaron baya, Habibu Yakubu, an dakatar da shi daga wasa a wannan karon.

“Yin wasa ba tare da muhimman ‘yan wasanmu kamar Ahmed Musa, Shehu Abdullahi, Rabiu Ali, da sauran su yana da matukar wuya. Ba abu ne mai sauki ba ga kowace kungiya, har da mu.

Amma, ina da yakinin cewa matasan ‘yan wasanmu sun koyi abubuwa da yawa daga manyan ‘yan wasa, kuma wannan dama ce gare su, su nuna kwarewarsu,” in ji Abdallah

Kano Pillars na fatan nasara a wasanta da Shooting Stars

Shugaba Tinubu ya taya iya murnar cika shekaru 90

GBV: Community, religious leaders pledge to work towards reducing menace in Niger