in

Kashim Shettima ya nemi hadin kai don magance matsalar makamashi

Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta samu ci gaban tattalin arzikin da ake buƙata ba sai an inganta bangaren makamashi. Ya ce rashin isasshen makamashi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana tattalin arzikin ƙasar bunkasa.

Shettima ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin majalisar tattalin arzikin Najeriya kan harkokin wutar lantarki da kuma yaƙi da cutar polio a fadar shugaban ƙasa. A cewarsa, inganta samar da makamashi zai taimaka wajen kawar da manyan cikas da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta.

Ya yi kira ga shugabanni da su ajiye bambancin siyasa gefe guda domin haɗa kai wajen magance matsalar makamashi.

“Lallai ba za a iya inganta tattalin arzikin ƙasar nan ba sai mun magance matsalar makamashi, sannan mu tabbatar dukkan ‘yan Najeriya suna samun isasshen makamashi,” in ji Shettima.

Ya jaddada cewa wannan lamari ba zai yiwu ba sai da cikakken goyon bayan shugabannin siyasa da ma’aikatun gwamnati.

Shettima ya nuna damuwa kan yadda 40% zuwa 70% na ƴan ƙasar ke fama da ƙarancin wutar lantarki.

Ya ce wannan matsala ce babba da ke hana miliyoyin ƴan Najeriya damar samun walwala da cin gajiyar arzikin ƙasar.

Sai dai ya bayyana kwarin guiwa kan kasancewar gwamnoni da sauran muhimman mutane a cikin kwamitin, inda ya ce hakan ya bashi tabbacin cewa za a samu nasara wajen magance matsalar makamashi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada muhimmancin samun hadin kai daga dukkan ɓangarori, yana mai cewa ci gaban Najeriya ya rataya ne a kan yadda za a magance matsalolin makamashi tare da tabbatar da cewa dukkan al’umma suna samun isasshen wuta.

Ya ce wannan aiki ne da ke buƙatar himma, haɗin kai, da kuma gaskiya daga dukkan masu ruwa da tsaki.

Kashim Shettima ya nemi hadin kai don magance matsalar makamashi

Gunmen kill guest in Benin nightclub, girl friend sustain gunshot injury, hospitalized

Mummunan hadari ya kashe dalibai a jihar Kogi