Komishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya kai ziyarar ban girma ga sabon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG) na Zone 1, AIG Ahmed Ammani, a ofishinsa da ke Zone 1 Headquarters.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a Kano ya wallafa.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, CP Salman Dogo Garba ya taya sabon AIG Ahmed Ammani maraba da zuwa Kano, tare da bayyana jajircewar rundunarsa wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
Ya ce rundunar ta samu nasarori wajen yaki da ‘yan daba (Daba) da sauran laifuka masu tada hankalin jama’a ta hanyar amfani da dabarun hadin gwiwa da Zone 1 Headquarters.
A nasa ɓangaren, AIG Ahmed Ammani ya yaba wa CP Dogo bisa irin koƙarin da yake yi wajen tabbatar da tsaro a Kano.
Ya kuma yi kira da a kara mai da hankali kan musayar bayanai da haɗin kai tsakanin Zone 1 da rundunar ‘yan sandan Kano domin tabbatar da zaman lafiya da magance kowanne irin barazanar tsaro da ka iya tasowa.
Komishinan ‘yan sanda na jihar Kano ya ziyarci sabon AIG na zone 1