Wata babbar kotu da ke zamanta a Jihar Jigawa ta yanke wa wani miji da mata, da wasu yan uwan matar biyu namiji da mace hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Birnin Kudu ne ya yanke hukuncin bayan ya samu waɗanda ake tuhumar da laifin kashe wata mata mai suna Salamatu Musa mai shekara 30 bayan sun yi zarginta da maita.
Kotun ta yanke hukuncin a Larabar nan, a shari’ar da aka shafe tsawon lokaci tun bayan kama waɗanda lamarin ya shafa a shekarar 2019.
Bayanai sun ce waɗanda aka yanke wa hukuncin waɗanda mazaunan garin Kwan-Dole na Ƙaramar Hukumar Malam Madori sun lakaɗa wa Salamatu duka da itace bayan sun yi zargin ta lashe musu ɗansu.
Mai shari’a Birnin Kudu ya ce waɗanda abun ya shafa suna da kwanaki 90 su ɗaukaka ƙara.
Kotu a jigawa ta yankewa miji da mata da ya uwan su hukuncin kisa