in

Kotun Borno ta yanke wa Mama Boko Haram da wasu hukuncin shekaru 5 a kurkuku

Babbar Kotun Jihar Borno da ke zama a Maiduguri ta yanke wa Aisha Wakil, wadda aka fi sani da “Mama Boko Haram,” tare da wasu mutum biyu hukuncin shekaru 15 a gidan yari saboda zamba ta naira miliyan 6 a cikin cinikin mota.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa da kuma zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya ta bayyana hakan a ranar Litinin, tana mai cewa an yanke wa Aisha Wakil tare da Manajan Shirin ta na gidauniyar Complete Care and Aid Foundation, Tahiru Saidu Daura, da Daraktan Ƙasa, Lawal Shoyode, hukunci bayan an same su da laifin karɓar mota kirar Toyota Camry na shekarar 2012 daga wani mai ƙorafi ta hanyar zamba da ƙarya.

An sake gurfanar da su uku a watan Satumban 2020 kan tuhumar laifuka hudu da suka haɗa da haɗa kai, yaudara, da bayar da bayanan ƙarya, inda suka musanta aikata laifukan.

Bayan doguwar shari’a, Mai Shari’a Aisha Kumaliya ta yanke wa kowannen su hukuncin shekaru biyar a kurkuku a ranar Alhamis.

A lokacin shari’ar, masu gabatar da ƙara, Mukhtar Ahmed da Shamsudeen Saka, sun gabatar da shaidu guda uku tare da miƙa wasu takardu a matsayin hujja.

Mai Shari’a Aisha Kumaliya ta yanke hukunci a gefen masu ƙara, inda ta yanke wa waɗanda ake tuhuma hukuncin shekaru biyar a gidan yari kowannensu, ba tare da zaɓin biyan tara ba.

Kotun ta kuma umarci waɗanda ake tuhuma su biya mai ƙorafi diyyar naira miliyan 3.5. Idan sun kasa cika wannan umarni, za a ƙara yanke musu hukuncin shekaru biyar a gidan yari kowannensu, in ji alkaliyar.

Sanarwar EFCC ta bayyana cewa waɗanda ake tuhuma ba su sayi motar kamar yadda aka yi yarjejeniya ba, kuma ba su ma mayar da ita ga mai ƙorafi ba, wanda hakan ya kai ga yanke musu hukunci.

Kotun Borno ta yanke wa Mama Boko Haram da wasu hukuncin shekaru 5 a kurkuku

Yahaya Bello’s co-defendant, Umar Oricha gets N300M bail with two sureties

Transfer: Awaziem swaps club in MLS