in

Ku samar da kaya masu inganci ko ku rasa lasisin ku – SON

Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON ta yi kira ga masana’antu da su tabbatar da cewa kayayyakin da suke samarwa suna bin ka’idojin Ma’auni na Masana’antu na Najeriya (NIS), ko kuma su fuskanci rasa lasisin su.

Shugaban Hukumar SON, Dakta Ifeanyi Chukwunonso Okeke, ya yi wannan kiran yayin bikin bayar da takardun shaidar cika ka’ida ga kamfanoni 52 da suka cika ka’idojin MANCAP a Kano.

Da yake wakiltar shugaban, Ko’odinetan Hukumar a Kano Office II, Dakta Ado Ibrahim, ya ce, “Takardar shaidar MANCAP ba kawai wata alama ce ta karramawa ba, amma tabbaci ne ga masu amfani da kayayyakin cewa an gudanar da gwaje-gwaje sosai a kansu don tabbatar da ingancinsu.”

Shi ma da yake magana, Ko’odinetan Hukumar Kano Office I, Roger John, ya gargadi kamfanonin da suka samu takardun shaida da su ci gaba da bin ka’idojin, ko kuma su fuskanci barazanar rasa takardun shaidarsu.

Ku samar da kaya masu inganci ko ku rasa lasisin ku – SON

Wike ya kwace mallakin filayen Buhari, Abbas, Akume da wasu fitattun mutane 759

Kotu ta umarci gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya diyyar 8.5bn kan rusa Daula otel ba bisa ka’ida ba