in

Kudirin gyaran haraji: Za mu tuntubi mutanen mu – Sanatocin Kudu maso Gabas

Kungiyar wakilan Kudu maso Gabas a majalisar dattijai ta ce ba ta adawa da kudirin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

Tinubu ya bukaci majalisar dokoki ta ƙasa da ta duba kuma ta amince da kudirin a watan Oktoba, amma an fuskanci ƙalubale daga gwamnonin Arewa da wasu ‘yan majalisar dokoki.

Saboda haka, kwamitin tattalin arzikin ƙasa (NEC) ya bukaci Tinubu ya janye kudirin domin a sake yin shawarwari, amma ya ƙi.

Yanzu kudirin ya na matakin sauraron ra’ayoyin jama’a a zauren majalisar bayan ya wuce karatu na biyu.

Da yake magana da manema labarai bayan taron caucus da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, Enyinnaya Abaribe, shugaban kungiyar, ya ce wakilan Kudu maso Gabas suna son a yi kara tuntuba game da kudirin.

“Dole ne mu yi shawara da al’ummominmu a fadin mazabu 15 na yankin… tare da gwamnatocin jihohinmu da sauran muhimman masu ruwa da tsaki,” in ji Sanatan da ke wakiltar Kudu ta Abia.

“Mun karanta kudirin kuma muna son mu raba iliminmu tare da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin Kudu maso Gabas domin samun tsarin da ya fi dacewa a cikin kudirin da za a amince da shi a ƙarshe.

“Ba ma adawa da kudirin, amma muna buƙatar yin shawara da mutanenmu,” in ji shi.

Kudirin gyaran haraji: Za mu tuntubi mutanen mu – Sanatocin Kudu maso Gabas

EPL: Hearing into Man City’s 115 charges concluded

Gwamnatin Katsina za ta kashe N36bn a gina katafariyar hanya