Kungiyar Alkalai ta kasa (MAN), reshen jihar Cross River, ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani bayan kasa cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.
An fara yajin aikin ne a yau, Litinin, 9 ga Disamba, 2024, inda aka umarci dukkan alkalan jihar da su daina gudanar da duk wani aikin ofis, ciki har da zaman kotu, har sai wani karin bayani ya zo.
Wannan bayanin yana cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar na reshen Cross River, Godwin Onah, da Sakatare Janar, Solomon Abuo, suka sanya wa hannu, kuma aka gabatar wa manema labarai jiya a Calabar
Jaridar DAILY POST HAUSA ta ruwaito cewa ma’aikatan shari’a sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnati a ranar 5 ga Nuwamba, 2024, don gargadin fara yajin aiki a ranar 27 ga Nuwamba.
To sai dai har kawo wannan lokaci ba a aamu sansantawa tsakanin kungiyar da bangaren gwamnati ba.
Sun fara yajin aiki na gargadi na tsawon kwanaki uku domin jaddada bukatunsu guda takwas ga gwamnatin Bassey Otu
Kungiyar alkalai ta tsunduma yajin aiki