Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP ya fara gudanar da wani zama na gaggawa a Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana abinda za a tattauna a taron ba, rahotanni sun nuna cewa halin da jam’iyyar ke ciki da kuma shirin gudanar da taron NEC za su kasance a kan gaba.
Idan za a iya tunawa, rikicin shugabanci ya lullube PDP, sannan akwai batun matsala da ake samu tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Kwamitin amintattu na PDP ya shiga taron gaggawa