in

Kwamitin haƙar ɗanyen mai ya nuna takaici akan jinkirin hakar mai a Kolmani

Kwamitin haƙar ɗanyen mai na hukumar tattara kuɗaɗen shiga da hada-hadar kuɗi (RMAFC), ya koka da jinkirin da ake samu wajen haƙar ɗanyen man fetur a Kolmani.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ziyarar duba yanda aikin ke tafiya kwamishinan gwamnatin tarayya na RMAFC, Injiniya Hassan Mahmoud ya nuna takaicin kan alaƙar kamfani Sterling Global, da al’ummar yankin na samar musu da ci gaba wanda tun shekaru biyu da suka gabata aka ƙaddamar da aikin haƙo man a Kolmani, wanda shi ne na farko a Arewacin Nijeriya.

Idan ba a manta ba a ko a kwanakin baya Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya tattauna da kamfanin NNPC, kan ci gaba da aikin haƙo man na Kolmani.

Kamfanin mai na NNPCL, tare da haɗin gwuiwar kamfanin New Nigeria, ne dai suka gano rijiyoyin mai guda biyu da suka wa laƙabi da OPL809 da kuma OPL810, a garin Kolmani, wanda aka yi hasashen za a samu kusan ganga biliyan ɗaya na ɗanyen mai kuma ana sa ran zai ɗore har zuwa shekarar 2060 inda NNPC, ya sha alwashin ci gaba da aikin amma a yayin ziyarar ba a ga alamar hakan ba.

Kwamitin haƙar ɗanyen mai ya nuna takaici akan jinkirin hakar mai a Kolmani

‘No crisis in NNPP’ – South-South state chairmen

Shugaban Jamus, Steinmeier ya kawo ziyarar aiki Najeriya