in

Kwara: An rage mukamin wata malama sakamakon zargin cin zarafin ɗan bautan ƙasa

Gwamnatin Jihar Kwara ta rage wa wata malama mukami sakamakon zargi da ake mata da cin zarafi ɗan bautan ƙasa da aka tura zuwa Makarantar Sakandaren Kasa ta Gwamanati, Kulende, Ilorin.

An ragewa Hajia Fatimoh Hamzat Nike mataki biyu daga cikin matsayin ta kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar a Ilorin daga hannun Kwamishinan Ilimi da Ci gaban Albarkatun Dan Adam, Hajia Sa’adatu Modibbo Kawu, da Shugaban Hukumar Koyarwa ta Jihar Kwara, Mallam Bello Tauheed Abubakar.

“Kwamitin bincike da aka kafa kan lamarin ya same Hajia Hamzat Fatimoh Nike da laifi na yin fada a kan aiki, amfani da kalmonin da basu dace ba, rashin biyayya, da kuma nuna rashin girmama uniform ɗin ɗan kasa.”

“Halin da ta nuna ya sabawa dokokin ayyukan gwamnati, don haka an rage mata matsayi biyu daga mukaminta.

“Haka kuma, za a canja mata makaranta daga inda take yanzu, sannan za ta fuskanci zaman shawarwari,” inji sanarwar.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa irin wannan cin zarafi ba za a lamunta da shi ba a kowane yanayi.

Kwara: An rage mukamin wata malama sakamakon zargin cin zarafin ɗan bautan ƙasa

EPL: Petit names one team that can catch Liverpool amid title race

APC chieftain raises legal concerns over Supreme Court verdict on lottery commission