in

LP ta kaddamar da kwamitin sulhu a Katsina

Jam’iyyar LP reshen jihar Katsina ta kaddamar da wani kwamitin mutum goma sha biyu a ranar Juma’a.

Kwamitin zai gyara rashin jituwa da ke tsakanin shugabannin jam’iyyar da mambobi bayan an yi zaɓen 2023.

A jawabin sa kafin bikin kaddamarwar da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Katsina, Shugaban LP na Jihar, Kwamared Ibrahim Musawa, ya yaba wa shugaban jam’iyyar na ƙasa bisa ƙoƙarin haɗa shugabannin jam’iyyar da mambobi don aiki tare.

Ya bayyana cewa wannan haɗin kai zai zama matakin nasara a zaɓen 2027 da ke tafe.

Musawa ya kuma bayyana cewa jam’iyyar na shirin samar da tsarin da zai tabbatar da cewa haƙƙinta ba zai sake salwanta ba a zaɓen 2027.

Ya sake nanata aniyar jam’iyyar ta tabbatar da sauya rayuwar al’umma ta hanyar kawo daidaito da gaskiya a cikin shugabanci a ƙasar.

 

LP ta kaddamar da kwamitin sulhu a Katsina

Police arrest two for vandalizing Bauchi Govt projects, recover stolen properties

Nigeria long overdue for tax reforms — FG