in

Ma’aikatan ruwa sun tsunduma yajin aiki a Kano

Ma’aikatan hukumar ba da ruwan sha ta jihar Kano, sun tsunduma yajin aikin sai babatagani daga safiyar yau Talata 10 ga Disambar 2024.
Wata sanarwa da kungiyar ma’aikatan ta futar ta umarci su da su rufe ofisohinsu har zuwa lokacin da zasu sami umarnin yanje yajin aikin.
Wata majiya daga ma’aikatar ta tabbatarwa da DAILY POST HAUSA cewa batun karin sabon albashi ne ummul aba’isin tafiya yajin aikin.
Majiyar tace ma’aikatan basu ga albashin su na watan Nuwamba ba, amma kwatsam a safiyar Talatar nan, sai aka tura musu tsohon albashi, abinda ya ta da hankalin ma’aikatan.
Bayanai sun nuna tun da rana aka rufe kofar ma’aikatar dake Kofar Nassarawa, rahotanni na cewa kungiyar kwadago ta jihar Kano ta shiga lamarin domin ganin an samu maslaha.

Ma’aikatan ruwa sun tsunduma yajin aiki a Kano

Senate moves to end exportation of raw materials, boost local industries

Sarki Sanusi II ya fadi hanyar warware matsalolin tattalin arziki