in

Mafi qarancin albashi: Ma’aikata sun rufe Kaduna, Nasarawa

Ma’aikata a jihohin Kaduna da Nasarawa, a ranar Litinin sun fara yajin aikin gargadi na mako guda domin neman a aiwatar da sabon mafi karancin albashi na kasa da kuma gyara sakamakonsa.

A jihar Nasarawa an rufe ofisoshin gwamnati da suka hada da majalisar dokokin jihar da kotuna da ma’aikatu.

Comrade Ismaila Okoh, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a Nasarawa, ya ce yayin da gwamnati ta yi alkawarin biyan mafi karancin albashi na N70,500, amma ta kasa samar da yarjejeniyar a rubuce.

Ya jaddada shirin ma’aikata na ci gaba da yajin aikin idan gwamnati ba ta dauki mataki ba

A jihar Kaduna jami’an kungiyar sun kulle sakatariyar jihar, harabar kotuna da sauran ofisoshin gwamnati.

Kungiyoyin NLC da Trade Union Congress (TUC) sun bayyana gazawar gwamnati wajen aiwatar da gyaran ma’aikata duk da biyan mafi karancin albashi na N72,000.

Mafi qarancin albashi: Ma’aikata sun rufe Kaduna, Nasarawa

Don’t milk Nigeria to death – Obi of Onitsha tells politicians

Osun 2026: Adisa declares interest in governorship race under APC