in

Majalisa za ta binciki ayyukan kwastam

A ranar Laraba, Majalisar Wakilai ta yanke shawarar bincikar ayyuka da harkokin hukumar kwastam ta kasa a dukkan iyakokin Nijeriya, tare da mai da hankali kan ayyukan fatauci, da kuma rahotannin cin zarafi.

An cimma wannan matsaya ne bayan amincewa da kudirin da Sesi Whingan ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.

Yayin gabatar da kudirin, Whingan ya bayyana cewa, bisa ga sashe na 4 (b, e, da f) na dokar hukumar kwastam ta 2023, hukumar tana da alhakin tattara kudaden shiga, hana fatauci da damfara, da kuma tabbatar da tsaron iyakokin Nijeriya.

Ya ce an samu rahotannin cin zarafi, ciki har da wani lamari a kan hanyar Badagry-Seme a ranar 1 ga Disamba, 2024, inda jami’an kwastam tare da sojoji suka yi wa wasu masu sufuri biyu, Taofeek Olatunbosun da Rafiu Abdelmalik, duka.

Whingan ya jaddada cewa an zargi mutanen biyu da kokarin fatauci, wanda hakan ya jawo rikici wanda sai da mazauna yankin da taimakon yan sanda suka shiga tsakani.

Dan majalisar ya yi karin haske cewa fasakwauri yana da mummunan tasiri ga tattalin arziki, ciki har da lalata masana’antun cikin gida, rage kudaden shiga na gwamnati, da kuma kawo kayan da ba su da inganci a kasuwa.

Majalisar ta umurci Kwamitin Kwastam da Haraji tare da Kwamitin Tsaro su binciki ayyukan Hukumar Kwastam a iyakokin Nijeriya, tare da mai da hankali kan ayyukan fasakwauri, zargin hannu da ake wa wasu jami’an hukumar, da rahotannin cin zarafi, sannan su gabatar da rahoto cikin makonni shida don daukar matakin doka.

Hakazalika, majalisar ta umarci kwamitocin tsaro da kwastam su binciki rawar da sojoji ke takawa wajen tallafawa jami’an kwastam, domin tabbatar da cewa ayyukansu suna kan tsarin doka da kare hakkin bil’adama.

Majalisa za ta binciki ayyukan kwastam

Juventus ta doke Man City

Championship: Moses thankful over Luton Town chance