Majalisar Dattijai ta kafa kwamitin da Sanata Abba Moro (PDP, Benue Kudu) ke jagoranta domin duba wuraren da ake da takaddama a cikin kudirin gyaran haraji,.
An umarci kwamitin ya duba wuraren tare da ba da rahoto ga zauren majalisar kafin sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudurin.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Barau I Jibrin (APC, Kano Arewa), ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisa a ranar Laraba.
Barau, wanda ya jagoranci zaman, ya ce akwai sabani kan kudurin, kuma an bai wa kwamitin alhakin tattaunawa da Antoni Janar na Tarayya (AGF), bangaren zartarwa, da sauran masu ruwa da tsaki.
A ranar 3 ga Oktoba, 2024, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Tarayya da kudirorin gyaran haraji guda hudu, a wata wasika da Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Tajuddeen Abbas, suka karanta yayin zaman majalisar daban-daban.
Tinubu ya ce kudirin zai karfafa hukumomin kudi na Najeriya, tare da bayyana cewa suna cikin manufofin ci gaban gwamnatin sa don kasar.
Sai dai, ‘yan Najeriya, ciki har da gwamnoni, sarakunan gargajiya, kungiyoyin farar hula, wasu ‘yan majalisa, da sauransu, sun nuna rashin amincewa da kudirin.
Majalisar dattijai ta kafa kwamitin duba kudurin haraji