Majalisar dattijai ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da duba kudirin dokar haraji, tana mai cewa ba a dakatar da wani bangare ko janye shi ba.
Shugaban majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana hakan yayin zaman majalisa ranar Alhamis, yana mai cewa majalisar tana ci gaba da sauke nauyin da aka dora mata na kare muradun ‘yan Najeriya.
Bayan wata doka da shugaban marasa rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar, Akpabio ya musanta rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa an dakatar da tattaunawa kan kudirorin ko an janye su.
Ya jaddada cewa, “Ba za a takura majalisar dattawa ba. Kowanne gyara da muka tabbatar zai amfanar da ‘yan Najeriya za mu ci gaba da shi. Wadannan kudirori na dauke da tanade-tanade da ke kare muradun jama’a.”
Shugaban marasa rinjaye, a nasa bangaren, ya gargadi al’umma da su guji yarda da bayanai na karya daga kafafen sada zumunta da rahotannin kafafen yada labarai, yana mai cewa, “Ba mu dakatar ko janye tattaunawa kan kudirin gyaran haraji ba. Duk wani yunkuri na takura wa majalisar dattajai ba na dimokuradiyya ba ne.”
Majalisar dattijai ta musanta dakatar da kudirin dokar haraji