Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa, Bola Tinubu ya umarci Ministan Kudi, Wale Edun ya saki dukkanin asusun kudaden shirin tallafawa alumma cikin sa’oi 72.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne a zamanta na yau Talata ,3 ga watan Nuwanban 2024.
Amincewa da kudirin da mataimakin shugaban majalisar ya gabatar da goyon bayan yan majalisu 20.
Majalisar ta ce sakin asusun zai bada damar fara aiwatar da shirye-shiryen hukumar.
Shirin tallafin ma’aikatar jinkai da kare afkuwar bala’oi ya gamu da cikas ne bayan an zargi shugabannin hukumar da almundahana, abinda ya janyo aka dakatar da shirin aka kuma rufe asusun hukumar
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnati ta sakarwa hukumar ba da tallafi mara