in

Majalisar wakilai ta bukaci ma’aikatar sufuri da su gudanar da bincike a kan yawaitar hadurran kwale-kwale

Majalisar Wakilai ta bukaci Ma’aikatar Tattalin Arzikin Ruwa da Ma’aikatar Sufuri da su gudanar da kwakkwaran bincike kan yawaitar hadarran kwale-kwale a Najeriya.

Wannan zaman ya biyo bayan wani kudiri na gaggawa na kasar wanda ya ja hankali kan hatsarin kwale-kwale a jihar Kogi da ya rutsa da fasinjoji sama da 160, inda aka ceto mutane 24, da kusan 54 ne aka tabbatar da suka rasa rayukansu.

Hon. Unyime Idem wanda ya gabatar da kudirin, ya nuna damuwarsa kan yadda yawaitar hadurran kwale-kwale a baya-bayan nan ya haifar da damuwa game da tsaron magudanan ruwa na Najeriya da kuma bukatar daukar matakan gaggawa.

Majalisar ta kuma bukaci hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya, NIMASA da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) da su aiwatar da ka’idojin tsaro da tabbatar da bin ka’idojin ruwa na kasa da kasa.

Majalisar wakilai ta bukaci ma’aikatar sufuri da su gudanar da bincike a kan yawaitar hadurran kwale-kwale

Reps direct CBN to halt retirement of 1000 staff pending investigation

105 persons lost 46 shops, stalls in Damaturu market inferno – SEMA